Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (ABNA) ya bayar da rahoton cewa: majiyoyin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun kwashe sojojin da suka samu raunuka sakamakon wani mummunan yanayin artabu da aka samu a garin Khan Yunus, a daidai lokacin da ake samun rahoton wani sabon harin kwantan bauna da sojojin mamaya na Isra'ila suka fada a yankin. A halin da ake ciki kuma, sojojin kai wasu sabbin hare-hare ta sama a wasu yankuna a zirin Gaza, lamarin da ya yi sanadin shahada da jikkata.
Shafin yanar gizo na Hadashot Hamot ya bayar da rahoton cewa, an gwabza kazamin fada a Khan Yunus, inda ya bayyana cewa, jiragen yakin sun kutsa kai a wani yanki da sashen injiniyoyi ke aiki, a ci gaba da yunkurin saukar jirage masu saukar ungulu da aka tanada domin kwashe wadanda harin ya ritsa da su.
Kafofin yada labaru sun kuma bayar da rahoton faruwar mummunan lamari mai wahala ga sojojin Isra’ila, lura da cewa jirage masu saukar ungulu na soji sun kwashe sojojin da suka jikkata zuwa asibitocin Isra'ila.
Tare da rahotannin munin lamarin, wakilin gidan talabijin na Aljazeera ya ba da rahoton hare-haren bindigogi da hare-hare ta sama, da kuma tashin jiragen sama marasa matuka da tankokin yaki a arewa maso yammacin Khan Yunis.
A ranar Talatar da ta gabata ne aka kashe jami’ai da sojoji 6 na Isra’ila a wani harin kwantan bauna da aka kai a Khan Yunis wanda dakarun Izzaddin Qassam suka yi ikirarin hakan.
Sojoji da dama ne suka kone kurmus bayan da wani mayakin Izzaddin Qassam ya jefa bam a cikin wata motar sulke. Wannan harin kwantan bauna dai ya janyo kiraye-kirayen da aka yi a kasar yahudawan sahyoniya da su dakatar da yakin da suke yi a zirin Gaza.
Sumamen Sojojin Isra’ila Yana Ci Gaba Da Gudana A Gaza
A halin da ake ciki kuma sojojin mamaya na Isra'ila sun kai wani samame da sanyin safiyar Juma'a a wasu yankuna da dama a zirin Gaza, inda suka sake kai hari kan mutanen da ke neman agajin abin zasu kashe yunwarsu da shi
A cewar wakilin gidan talabijin na Aljazeera, ya nakalto daga Asibitin Al Awda, wani bafalasdine daya yayi shahada, yayin da wasu biyar suka jikkata sakamakon farmakin da aka kai kan fararen hula da ke jiran agaji a kudancin yankin Wadi Gaza da ke tsakiyar zirin Gaza.
Majiyar Falasdinawa ta bayar da rahoton cewa, sojojin Isra’ila sun yi ruwan wuta a yankunan Zeitoun da Shuja'iyya a kudu da gabashin birnin Gaza.
Jiragen saman Isra'ila sun kuma kai farmaki a yankunan Jabalia da Beit Lahia da ke arewacin zirin Gaza.
A kudancin zirin Gaza, jiragen saman Isra'ila sun kai farmaki kan gidajen da ke tsakiyar Khan Yunis. Majiyoyin Falasdinawa sun ba da rahoton shahadar wani likita da yayan sa sakamakon harin bam da aka kai a wata tanti a yankin Al-Mawasi da ke yammacin birnin.
Majiyoyi a asibitocin Gaza sun ba da rahoton cewa an kashe Falasdinawa 72 a ranar Alhamis, ciki har da mutane bakwai daa aka kash su a kusa da cibiyoyin rarraba kayan agaji.
An rarraba shahidan a yankuna da suka hada da Khan Yunis da Rafah a kudu, Deir al-Balah a tsakiya, da birnin Gaza da Jabalia a arewa.
Bayan sauya yarjejeniyar tsagaita bude wuta a watan Maris din da ya gabata, gwamnatin Sahayoniyya ta mamaye yankin Gaza ta ci gaba da kai munanan hare-hare a zirin Gaza. Tun daga wannan lokacin, kimanin Falasdinawa 6,000 ne aka kashe tare da jikkata sama da 20,000, a cewar sabbin bayanai daga ma'aikatar lafiya a zirin Gaza.
Your Comment